Abu na farko da zan fara yi akan kujerar mulki – Atiku


Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sake jaddada matsayar sa ta tabbatar da sauya fasalin kasar nan ta Najeriya tare da yi mata garambawul yayin nasarar sa zaben kasa da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

A jiya Litinin dan takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar da tabbacin sa na sauya fasalin Najeriya a matsayin aiki na farko da zai gudanar da zarar ya karbi mulkin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu.

Atiku ya sake bayar da wannan tabbaci ne a jiya Litinin cikin jawaban sa ga magoya baya yayin taron sa na yakin zabe da ya gudanar a harabar filin wasanni na Adamite Amiesimaka da ke birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Wazirin Adamawa tare da abokin takarar sa, Peter Obi da kuma sauran jiga-jigai na jam’iyyar PDP, sun sha alwashin riko da doka tare da yiwa kundin tsarin mulkin kasar nan da’a a kowane yanayi yayin da suke rike da akalar jagorancin kasar nan.

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like