Abin Kunya: Ɗan Majalissa ya Cinye Kuɗin Zakkah A Masallaci


Rt hon. Abdullahi balarabe salame Dan Majalisa ne Mai wakiltar kananan Hukumomin Gwadabawa da Illela
Daga Jihar Sokoto A Majalisar Tarayyar Nageriya
Dan Majalisar Dai Yana Zaune A National Assembly Quarters kusa da Masallacin Apo Zone A, Abuja

Hon Salame Ya Kasance Shine Mai Rike Da Mukamin Ma’ajiyin kudi Na Masallacin Haka Yasa Duk Wani Sadaqa Ko zakkah Da Ake Kawowa ga Masallacin Ake Mikasu A Hannun Hon Salame

A Makon Daya Gabatane Dai Aka Kawo Zakkah Zuwa Ga Masallacin Domin Rabama Mabukata Amma Abin Mamaki Ace Dan Majalisa maici Yanzu Kuma Wanda Ya Taba Rike Mukaddashin Gwamnan Jihar Sokoto A Lokacin Da wamako Ya samu matsala A Zaben 2008
Shine zai Cinye Kudin Mabukata Wa Yanda Suke Cike Da Bukatu Amma Ya Cinye Kudin Zakkarsu.

Hakika Duk Wanda Ya kasa Rike Amanar Masallacin To Hakika Zai Wahala Ya Iya Rike amanar al’ummarsa bil’hakki Da Gaskiya domin ya Rasa Mutuncin Shugabanci.

Sauran Wa’yanda Sukaci Kudin Zakkar Sun Hada Da
Tsohon Sanata Wato Sanata Dan sadau Zamfara

Da Tsohon Sanata Sani Kamba Daga Jihar kebbi

Yanzu Haka Dai Acikin Masu Rike Da Mukamin Masallacin Akwai Wa’yanda Basu Da Cin Yau Balantana Na Gobe Amma Kuma Dukda Haka su Salame Suka Handame Dukiyar Zakkah dukda Matsayinsu Na Masu Mulki

Dan Allah ku fadamin Ina Adalci A Nageriya?

Comments 2

Your email address will not be published.

You may also like