Abin Da ‘Yan Najeriya Ke Cewa Kan Yadda Za A Shawo Kan Matsalar Tsaro
Matsalar rashin tsaro a Najeriya musamman a yankin arewa tana ci gaba da hana jama’a barci cikin natsuwa ko kuma doguwar tafiya akan manyan hanyoyin kasar saboda rashin tabbas ga tsaron rayuka ko dukiyoyinsu sanadiyar ayyukan ‘yan bindiga.

Ko a ranar Larabar wannan mako, ‘yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyuka dake yankin sabon birni a gabashin cihar Sakkwato wadanda suka yi sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sa’idu Ibrahim Naino dan majalisar dokoki mai wakiltar yankin sabon birni a majalisar dokoki ta jihar Sakkwato ya ce ko kafin harin na wannan mako ‘yan bindiga sun kai farmaki a wasu garurwa.

Duk da cewa akwai jami’an soji da ‘yan sanda a yankin amma yanayin yadda suke karbar umurni kafin yin aiki yana mummunan tasiri ga shawo kan matsalar, sabanin yadda jama’ar yankin ke gani ga makwabtansu dake Jamhuriyar Nijar, a cewar wani mazaunin yankin na Sabon Birni Abdullahi Tsamaye.

Matsalar rashin tsaro dai na ci gaba da gurgunta al’amurra a Najeriya musamman a yankin arewa da ke fama da wasu matsaloli ko bayan matsalar tsaron.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.