Abin Da Masana Shari’a Ke Cewa Kan Hukuncin Da Kotu Ta Yankewa Farouk Lawal
A ranar Talata kotun ta zartar da hukuncin ga tsohon ‘dan majalisar saboda samun sa da laifin karbar toshiyar baki a shekarar ta 2012 daga Femi Otedola, wanda dan kasuwa ne mai hada-hadar albarkatun mai, domin ya wanke ko cire kamfaninsa daga jerin kamfanonin da gwamnati ke zargi da almundahanar kudaden albarkatun mai.

Shekaru 19 kotun ta yanke wa tsohon dan majalisar akan laifuka guda 3 da aka tuhume shi da su, amma daga baya suka rikide suka zama 7.

A cewar Dr. Nasiru Adamu Aliyu SAN lauya ne mai zaman kansa a Kano, laifukan a jere da kwanakin ne aka yi lissafinsu daga karshe kotun ta bada hukuncin shekaru 7 a jere maimakon 19.

Sai dai Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa na Jami’ar Bayero, Kano ya yi tsokaci ne akan makomar laifin da aka zargi Mr. Femi Atedola na cin amanar dukiyar kasa.

Ya kuma yi bayani cewa Faruk Lawal ya nema karbar kudin ne domin ya kama Otedola amma bai san cewa shiga Otedola ya yi niyyar kama Faruk saboda tambayar da ya yi masa ta kudin domin cire sunan kamfaninsa. Ya ce amma Daga karshe Faruk ne aka kama.

Ga alama dai lauyoyi da alkalai za su ci gaba da fafatawa akan wannan batu, domin kuwa ta yiwu Hon. Faruk Lawan zai daukaka kara zuwa kotu ta gaba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.