Abin Da Ma’abota Twitter Ke Cewa Kan Goyon Bayan Da Trump Ya Nunawa Najeriya
Masu ra’ayoyi wadanda sun yi fice a lamuran yanar gizo a Najeriya na bugun jaki da taiki ne a lokaci guda sabanin wadanda ba su shahara ba da ke daukar kafar ta ‘yan jari hujja ce.

Mai fafutuka Deji Adeyanju ya ce Twitter ta yi adalci wajen dakatar da shafin Donald Trump don haka ya ke murna in wata kasa ta dauki irin wannan mataki akan Twitter, kamar yadda Najeriya ta yi.

Shi ma ma’abocin yanar gizo dare da rana, George Onmonya Daniel da ke caccakar manufofin shugaba Bubari, ya ce bai yi mamakin matsayar da Trump ya dauka ba.

Amma a na sa bangaren, mawallafin jaridar yanar gizo ta “Daily Nigerian” Jafaar Jaafar na ganin Trump ya yi daidai, kamar yadda shugaba Bubari ya takawa Twitter birki biyo bayan goge sakonsa da yake ganin mai ma’ana ne.

Ministan labarun Najeriya Lai Muhammed ya ce kamfanin Twitter ya fara tuntubar Najeriya don sanin mataki na gaba da za a dauka wajen sasanta wannan rikici.

Gwamnatin Najeriya ta zargi dandalin wanda ke da mabiya sama da miliyan 39 a kasar, da ruruta wutar rikice-rikice a sassan kasar.

Kamfanin na Twitter ya haramta wallafa bayanai da ka iya ta da husuma ko nuna kyama ga wani ko wasu, ka’idar da ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya take.

Kusan mako guda kenan ana ta ka-ce-na-ce a Najeriya dangane da haramcin da hukumomin Najeriya suka saka wa kamfanin, matakin da ke shan suka a ciki da wajen kasar.

Hukumomin Najeriya sun ce matakin ya yi tasiri, yayin da wasu ke nuna akasin hakan, lura da cewa wasu na iya amfani da kafar VPN wajen shiga shafin.

Saurare cikakken rahoton cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg