Abin Da Kwararru Ke Cewa Kan Yadda Za A Inganta Tsarin Almajiranci A Najeriya
Fiye da shekara daya kenan da gwamnatoci a Najeriya suka daura damarar dakatar da almajiranci a jihohin su inda wasu jihohin irin Kaduna da Kano suka fara tura keyar almajirai jihohin su na asali wasu kuma suka soma shirin inganta tsarin maimakon korar almajirai.

Tun a wannan lokacin ne jihar Sakkwato wadda ke arewa Maso yammacin Najeriya take tsare-tsare na kwaikwayon tsarin almajiranci na kasar Indonesia don inganta tsarin a jihar.

Sai dai akwai tsare-tsare da dole sai an yi aiki da su kafin haka ta cimma ruwa a wannan shirin, abinda ya sa masana suka hadu suka tattauna akan tsare-tsaren.

Dokta Bala Muhammad na Jami’ar Bayero ta Kano na ganin cewa tamkar tsarin karatun boko, shi ma wannan tsarin dole sai an samar masa manhajar karatu a cewar Farfesa Muhammad Ibn Junaidu.

Masu kula da wannan tsarin dai sun kwashe sama da shekara daya suna fadakar da jama’a amfanin sa.

To ko me yasa ake son amfani da tsarin na kasar Indonesia? Muhammad Lawal Maidoki wanda yana cikin ayarin gwamnatin jihar da suka ziyarci kasar ta Indonesia don nazarin kwaikwayon tsarin na su ya bayyana cewa tsari ne mai mahimmanci na tarbiya ga dalibi wanda ya amfani kasar ta Indonesia da ya sa duk da yawan su muka yawanci musuilmai amma ba sa yawon bara.

Masu lura da al’amurra dai na nuna fargaban dorewar wannan shirin a gaba, koda ya samu nasara a matakin farko, saboda muddin ba dukan jihohi suka hadu wuri daya ga aiwatar dashi ba akwai yuwar kwarorwar almajirai daga wasu jihohi zuwa inda ake aiwatar da shirin abinda kan iya kawo nauyin gudanar dashi ga jihar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.