Abaribe ya zama Shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa ta 9


Sanata Eyinnaya Abaribe mai wakiltar mazabar kudancin jihar Abia a majalisar dattawa shine zai kasance sabon shugaban Marasa Rinjaye a Majalisar Dattawa ta 9.

An zabi Abaribe ne a wurin wani taro da ya gudana a gidan shugaban jam’iyar PDP na kasa ,Uche Secondus dake unguwar Maitama a Abuja.

Sanata Emmanuel Bwacha daga jihar Taraba shine zai kasance mataimakansa ya yin da sanata Philips Tanimu Aduda daga birnin tarayya Abuja zai kasance bulaliyar marasa rinjaye.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like