AAC ta kori Sowore


Jam’iyar AAC ta kori,Omoyele Sowore shugabanta na kasa daga jam’iyyar.

Sauran mutanen da abin ya shafa sun hada da wasu mutane 28 dake cikin kunshin shugabancin jam’iyyar a kasa.

Jam’iyar ta dauki wannan mataki a wurin babban taronta na kasa da yake gudana a otal din Rockview dake Owerri babban birnin jihar Imo.

Dr. Leonard Ezenwa shine mutumin da ya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban jam’iyar na kasa.

Hakan na zuwa ne bayan da wata babbar kotu dake Abuja ta bawa hukumar DSS izinin cigaba da tsare Sowore har tsawon kwanaki 45.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like