A Yau Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto Da Sir Abubakar Tabawa Balewa Suka Cika Shekaru 55 Da Rasuwa


A yau 15 ga watan Janairu Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da Sir Abubakar Tabawa Balewa suka cika shekaru 55 da rasuwa.

An kashe marigayi Sir Ahmadu Bello ne a ranar 15 ga watan Janairun shekarar 1966 a jihar Kaduna, inda shima marigayi Sir Abubakar Tabawa Balewa, shima aka kashe shi a ranar 15 ga watan janairun a jihar Legas.

Kafun a kashe su sun bada gudummuwarsu ga al’ummar yankin mu na Arewa dama kasar Nijeriya baki daya, mutane ne masu kishin yankinmu, masu son cigaban yankin mu dama kasar baki daya.

Muna musu Addu’ar Allah ya jaddada Rahama gare su, ya hada Fuskokinmu dasu a gidan Aljanna Firdausi Yaa Hayyu Yaa Qayyum. Amin


Like it? Share with your friends!

0

Comments 9

You may also like