A Kullum Da Tunanin Talakawa Nake Kwana – Buhari


Shugaba Muhammadu Buhari ya yi gaisuwa ga masu masaukin baki da sauran mukarraban Gwamnati.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da irin tarbar girmamawa da jama’ar jihar Jigawa suka yi masa, kan ziyarar aiki ta yini biyu da ya kawo tun jiya bisa amsa gayyatar gwamna Muhammad Badaru Abubakar..

Ya kuma yaba da yadda ya ga ayyukan noman suna cigaba da kankama a wannan jiha.

Daga karshe ya tabbatarwa ‘yan kasa cewa a kullum da tunanin mu yake kwana yake tashi kan halin da muke ciki.

Ya kuma jaddada cewa, Insha Allahu ba zai ci amanar al’umma ba, kuma da sanin sa ba zai bari a ci amannar al’ummar wannan kasa ba.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like