A karon farko an fara sayar da kayan adon Kirsimeti a kasar Saudiyya


An fara sayar da kayayyakin adon bikin Kirismeti a wani shagon dake birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

A baya mutane basu taba tunanin za a kawo irin wannan lokaci da za a rika sayar da irin wannan kayayyakin a kasar dake bin dokokin addinin musulunci sau da kafa.

An samu gagarumin wannan sauyi ne a kasar bayan da yarima mai jiran gado, Muhammad bin Salman ya kawo wasu sauye-sauye na mayar da kasar mai bin matsaikancin ra’ayin addini

Tuni ma dai wasu gidajen abinci suka fara tallan garabasa ga kwastomomi domin bikin murnar ranar masoya ta duniya da ake kira Valentine Day da za a yi cikin watan Fabrairu.


Like it? Share with your friends!

-2

Comments 7

You may also like