Dan wasan Hausa mai yin fina-finan barkwanci wato Ali Artwork wanda aka fi sani da Madagwal ya mayar da Abdullahi Abbas shugaban jam’iyyar na Kano martani kan kalaman da yayi game da zaben shekarar 2023.

Abbas ya yi ikirarin cewa za su murde zaben 2023 kuma babu abin da aka isa ayi ya kuma kara da cewa za su daki yan kwankwasiyya matukar suka yi musu ba dai-dai ba.

A cikin wani fefan bidiyo da ya wallafa Madagwal ya ce su magoya bayan Kwankwaso mutane ne masu son bin dauka da kuma bin tanade-tanaden tsarin mulki.

Ya kara da cewa tarbiyya da aka basu ba ta zagin jama’a ba ce face ta girmama mutane.

Ya ce matuƙar shugaban ya cigaba da irin wadancan kalamai to tabbas za su saka kafar wando daya da shi.