Gwamnonin jam’iyar APC sun yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban kasa, Gudluck Jonathan a Abuja da yammacin ranar Juma’a.

Babu dan jam’iyar PDP ko mutum guda a wurin taron.

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni wanda shine shugaban kwamitin riko na jam’iyar APC shi ya jagoranci gwamnonin APC ya zuwa gidan Jonathan dake Abuja.

Dave Umahi wanda a yan kwanakin nan ya koma jam’iyar APC daga PDP,gwamnan Jigawa, Badaru Abubakar, da kuma shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyar APC, Atiku Abubakar na daga cikin wadanda aka ga fuskokinsu a wurin taron.

Babu cikakken bayani kan abin da suka tattauna sai dai wata majiya ta bayyana cewa ganawar bata rasa nasaba da zaben shugaban kasa na 2023.