2019: Ranar Asabar mai zuwa Buhari zai fadi zabe – Uche Secondus


Labari ya iso gare mu cewa Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya watau PDP yace shugaba Muhammadu Buhari zai fadi zaben da za’ ayi a karshen makon nan

Shugaban jam’iyyar PDP din na kasa baki daya, Prince Uche Secondus ya bayyana cewa a Ranar Asabar dinnan ne jama’an Najeriya za su zabi jam’iyyar PDP inda za a tika APC mai mulki dakasa a zaben shugaban kasa da za ayi.

Uche Secondus yayi wannan jawabi ne a shafin sa na sadarwa na Tuwita bayan ganin irin lale marhabin din da dinbin jama’a su ka yi wa ‘dan takarar PDP na shugaban kasa watau Atiku Abubakar a jihar Kano jiya Ranar Lahadi.

Secondus yace kwanakin baya mutane sun amsa kiran Atiku Abubakar a Katsina inda anan shugaban kasa ya fito, sannan kuma ya ga yadda Kanawa kwan-su da kwarkwatar su, su ka ba jam’iyar hamayyar goyon baya a jiya.

Shugaban na PDP ya Kara da cewa irin watsi da jama’ar Legas su kayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna cewa babu shakka PDP za tayi nasara yayin da shi kuma shugaba Buhari zai koma gida Daura.


Like it? Share with your friends!

2
83 shares, 2 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like