2019: An Nemi Jam’iyyar PDP Ta Sauya Dan Takarar Shugaban Kasa


Daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Mista Stanley Osifo, ya yi barazanar tayar da zaune muddin jam’iyyarsa ta gaza wajen sauya dan takararta na kujerar shugaban kasa a yayin babban zabe na 2019, Atiku Abubakar.

Mun samu rahoton cewa, Mista Stanley ya bayar da wa’adin kwanaki 2 ga jam’iyyar kan ya gaggauta watsar da Atiku a matsayin dan takarar ta tare da yin kira kan sauya da wani sabon dan takara na jam’iyyar.

Osifo ya kuma yi barazanar gurfanar da jam’iyyar sa gaban Kuliya muddin ta gaza wajen tabbatar da wannan bukata da ya gindaya ta watsar da Atiku a matsayin gwanin ta na takara da kuma kiransa sake sabon dan takara na jam’iyyar .

Yayin ganawarsa da manema labarai cikin birnin Legas, Osifo ya bayyana cewa, dukkanin manema tikitin takara na jam’iyyar na da cikakken alhaki na samun dama tamkar ta Atiku da a cewar sa kowanen su ya mallaki takardun neman kudirin takara daidai da na Atiku.

Dan takarar da ya kasance haifaffen jihar Edo ya bayyana cewa , takaicinsa ya takaita ne kadai dangane da ya yadda ya zubawa Sarautar Mai Duka idanu wajen halarta tare da shiga cikin sahun tantance manema tikitin takara da jam’iyyar ta gudanar yayin zaben ta na fidda na gwani.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, jam’iyyar ta PDP ta gudanar da zaben ta na fidda gwanayen takarar cikin farfajiyar wasanni ta Adokiye Amiesimaka dake birnin Fatakwal na jihar Rivers a ranar 6 ga watan Oktoba da ya gabata.

A ranar Litinin data gabata ne dai , tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku, ya kaddamar da yakin neman zabensa na takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwar jam’iyyar PDP a jihar Sakkwato.


Like it? Share with your friends!

2
104 shares, 2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like