′Yan tawayen Chadi na son tsagaita wuta | Labarai | DWA cikin hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Faransa na AFP, shugaban ‘Yan Tawayen da ake wa lakabi da FACT Mahamat Mahadi Ali ya tabbatar da aniyarsu ta tsagaita wuta da cimma matsaya da gwamnati. 

Sai dai Mahadi Ali ya yi gargadin cewa idan har ana son ganin hakan dole sai bangaren sojojin Chadi shi ma ya tsagaita wuta, yana mai cewa ba za su zura ido su ga dakarun gwamnati na kashe su ba tare da sun rama ba.

Da yake mayar da martani a kan wannan batu, mai magana da yawun majalisar soji da ke mulkin Chadi ya ce sojoji na na yi wa mutanen na kungiyar FACT lugudan wuta ne saboda ‘yan tawaye ne kuma abin da hukuma za ta iya yi musu ke nan.

 
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg