Ɓarayi sun kashe ƴansanda 16 a Zamfara


Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa an kashe jami’anta 16 a musayar wutar da suka yi da gungun barayi a jihar ranar Alhamis.

Rundunar ta kuma bayyana cewa an samu nasarar ceto wasu ƴansanda 20.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, Muhammad Shehu kakakin rundunar ƴansandan jihar ya ce, babban sifetan ƴansanda na kasa, Ibrahim Idris ya kadu matuka da mutuwar jami’an wadanda ya bayyana a matsayin gwaraza.

Ranar juma’a ne rundunar ƴansandan jihar ta sanar da kashe barayi yan bindiga 104 a wani farmaki da ta kai musu a karamar hukumar Birnin Magaji dake jihar sai dai kuma rundunar ta yi shiru kan yawan mutanen da ta rasa.

Shehu ya ce wata tawagar jami’an tsaro na cigaba da sanya idanu akan maboyar bata garin.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like