Ƴansanda sun kashe mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da mutane a Taraba


Rundunar ƴansandan jihar Taraba ta ce jami’anta dake aiki a ofishin ƴansanda na Bali a ranar Lahadi sun kashe wasu mutane uku da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne da suka dade suna addabar al’ummomin Bali da Suntai dake karamar hukumar Bali ta jihar.

Kwamishinan ƴansandan jihar,David Akinremi shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Jalingo.

Akinremi ya ce wasu daga cikin masu garkuwar sun samu munanan raunuka lokacin da suke musayar wuta da jami’an ƴansanda yayin da suke kokarin yin garkuwa da mazauna wani gida dake kauyen Garwa.

” Kai daukin gaggawa da jami’an ƴansandan suka yi da kuma taimakon yan bijilante shi ya haifar da musayar wutar har ta kai ga kashe batagarin su uku yayin da ɗan bijilante guda daya ya samu rauni sakamakon harbin bindiga,” ya ce.

Ya kara da cewa an samu nasarar kwato bindigar AK-47 kirar gida guda daya, harsashi 9, wayoyin hannu guda biyu, kakakin sojoji, wukake da kuma wasu guraye.

Kwamishinan ya kara da cewa wasu daga cikin mutanen sun tsere da raunin harbin bindiga inda ya ce jami’an rundunar na cigaba da farautarsu.


Like it? Share with your friends!

-1
95 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like