Ƴansanda sun kashe barayi 9 a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna


Rundunar yan sandan Najeriya ta ce jami’anta sun kashe wasu mutane 9 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne ya yin wata musayar wuta a dajin Akilbu dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Mai magana da yawun rundunar,Frank Mba shine ya bayyana haka inda ya ce biyu daga cikin gungun barayin sun tsere da raunin harbin bindiga.

Ya ce kokarin da ake na kakkabe bata gari dake addabar matafiya akan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya samu karin nasara ranar 10 ga watan Afirilu bayan da aka kwato bindiga kirar Ak-47 guda 6, harsashi 1,206 gidan zuba harsashi 7 da kuma kwanson harsashi guda 158.

Amma kuma ya ce daya daga cikin jami’an ƴansandan ya samu rauni sakamakon harbin bindiga kuma yanzu haka na samun kulawa a asibiti.


Like it? Share with your friends!

-1
78 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like