Ƴansanda sun kama yan fashi hudu a Bauchi


Rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane hudu da ake zarginsu da fashi da makami da kuma wasu yan sara suka su 60 a fadin jihar.

Anyi holin munanen da ake zargi ne a hedkwatar rundunar dake Bauchi.

A cewar mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,Kamal Datti Abubakar an samu wannam. nasara ne sakamakon cigaba da jajircewa da kwamishinan ƴansandan jihar,Habu Sani Ahmadu yake na raba jihar da bata gari.

An kama yan fashin ne a yankin Kofar Wambai dake cikin birnin jihar biyo bayan samun bayanan sirri da rundunar ta yi.

Mutanen sunyi fashin wata mota kirar Jeep daga hannun wata mata akan hanyar Abuja zuwa Jos.

Yan fashin da suka fada hannun jami’an tsaron sun hada da Audu Daniel mai shekaru 29 dan asalin jihar Benue da kuma John Samuel dan jihar Imo.

Datti ya kara da cewa a wani samame na daban rundunar ta samu nasarar kama yan Sara-Suka inda ta same su da adduna 11, wukake biyu da kuma kwalin kwaya 8.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like