Ƴansanda sun kama wani mutum dauke da sassan jikin bil’adama a Ekiti


Jami’an ‘yansanda a jihar Ekiti sun kama wani mutum mai shekaru 23 a wurin shingen binciken ababen hawa inda ake zarginsa da boye wani ɓangare na jikin bil’adama a cikin leda.

Mutumin da aka bayyana da suna Nifemi an kama shine ranar Asabar a Ijero-Ekiti dauke da konannun hannun mutum lokacin da yansanda suke tsayar da ababen hawa suna bincike.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa jami’an ƴansanda na caji ofis din Ejero-Ekiti sun tsaurara matakan tsaro a duk fadin karamar hukumar tun bayan da mazauna yankin suka samu wata wasika daga yan fashi da makami dake cewa za su fara kai hare kan al’ummar yankin.

Nifemi ya fada hannun ƴansandan ne dake gudanar da bincike inda ake zargin yana riƙe da jakar leda dake dauke da hannayen a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Okemesi inda zai kai wa wasu mutane.

Mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,DSP Caleb Ikechukwu ya tabbatar da faruwar lamarin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like