Ƴansanda sun kama wani kansila dake da hannu a kashe-kashen jihar Benue


Rundunar ƴansandan Najeriya ta kama karin wasu mutane 8 da ake zarginsu da hannu a rikicin jihar Benue.

Jimo Moshood, mai magana da yawun rundunar, ya bayyana cewa cikin mutanen da aka kama akwai Benjamin Tivfa, wanda kansila ne mai ci na mazabar Fidi dake jihar.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan da suka faru a jihar ta Benue cikin wannan shekara.

A sanarwar da aka fitar ranar Talata Moshood ya bayyana cewa kansilan ya amince da samarwa da wasu yan ta’adda makamai domin aikata aiyukan ta’addanci kan al’ummar jihar.

Sauran wadanda da aka kama sun hada da Victor Ganabe, Daniel Kyase, Adajo Tomza, Msugh Sengv, Julius Avan, Terkula Ideh da kuma Sunday Cheche dukkanin mutanen sun fito ne daga kananan hukumomi daban-daban dake jihar.

Ya ce wadanda ake zargin an kama su ne ranar 27 ga watan Yuni kuma sun kasance yan kungiyar dake tabbatar da bin dokar hana kiwo shanu a fili da gwamnatin jihar ta kafa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like