Ƴansanda sun kama shugaban CAF a Faransa


Ƴansanda a Paris babban birnin kasar Faransa sun kama,Ahmed Ahmed shugaban hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF.

A cewar jaridar Jeune Afrique, an kama Ahmed da karfe 8:30 na safiyar yau a otal din Beri dake Paris inda yake zaune gabanin babban taron hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da za a gudanar a birnin.

Kamen baya rasa nasaba da zargin barnatar da kudade da kuma aikata cin hanci rashawa da ya shafi wani kamfanin kasar Faransa mai suna Tactical Steel.

Kafin korarsa daga aiki cikin watan Afirilu,Amir Fahmy tsohon sakataren CAF ya zargi Ahmad da cin hanci da rashawa.

Fahmy cikin wasu takardun bayanai da ya aikewa da kwamitin bincike na hukumar FIFA ya zargin shugaban da jawowa hukumar karin kashe dala 830,000 sakamakon sayan kayayyaki daga kamfanin na Tactical Steel.

Ahmad ya kare kansa inda ya bada tabbacin cewa dukkanin matakin daka dauka anyi ne batare da kunbiya-kunbiya ba.


Like it? Share with your friends!

-1
58 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like