Ƴansanda sun kama mutane 4 kan sayarwa da man fetur ga masu garkuwa da mutane a Katsina


Jami’an ƴansanda a jihar Katsina sun kama wasu mutane uku da ake zargi da sayar da man fetur ga masu garkuwa da mutane da kuma barayi a jihar Katsina.

Mutanen da aka kama sun hada da Zaharadeen Masa’udu, Ibrahim Khalid, Najib Dayyabu and Halliru Yarima.

Da yake holin mutanen da ake zargi mai magana da yawun rundunar yansandan jihar,SP Gambo Isah ya ce an kama mutanen ne bisa dogaro da umarnin hana sayar da man fetur a wasu kananan hukumomi da ke fuskantar yawan garkuwa da mutane.

A cewarsa bayanan sirri da rundunar ta tattara su suka kai ga samamen da ya kai ga kama mutanen a kananan hukumomin Batsari da Dutsinma.

Ya kara da cewa mutanen sun kware wajen sayarwa, samarwa da kuma rarraba man fetur ga barayin.

Ya ce jarkuna 33 cike da manfetur da kuma wasu 24 da babu komai a ciki aka samu a wurin mutanen da ake zargi.

Amma kuma dukkanin mutane hudun da ake zargi waɗanda manajojin gidajen mansune sun musalta yin wani abu na daidai ba.

Zaharadeen ya ce ” an kama ni ne saboda mallakar jarkoki,” ya yin da shi kuma Ibrahim ya ce “muna sayarwa da manoma ne wadanda suke amfani da shi wajen noman rani.”


Like it? Share with your friends!

1
105 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like