Ƴansanda na zargin wani dan majalisar tarayya a Kano da hannu a kisan wasu mutane uku


Rundunar ƴansandan jihar Kano, na binciken dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Wudil/Garko, Muhammad Ali Wudil bisa zargin da ake masa da hannu a kisan wasu mutane uku a karamar hukumar Rano dake yankin Kano ta kudu

Aƙalla mutane uku aka kashe lokacin da jam’iyyar APC ta kaddamar da yakin neman zabenta a yankin mazabar majalisar dattawa na mazabar Kano ta kudu.

A wata sanarwa ranar Alhamis mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya ce rundunar ta tattara cikakken bayanai dake nuni da hannun dan majalisar a kisan kuma nan ba dadewa rundunar zata gayyaci dan siyasa.

A cewar Majiya rundunar ta gargadi da dan majalisar da kada ya halarci wurin taron saboda rahotanni tsaro da rundunar ta samu akansa amma yaki bin shawarar.

Amma yayi watsi da shawarar inda ya tafi wurin taron da yan daba har ta kai ga sun kashe mutane uku a wurin.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like