Ƴanbindiga a garin Abaji sun sace wani mutum mai shekaru 27


Wasu ƴanbindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun sace,wani mutum mai suna, Kabiru Sani dan shekara 27 mazaunin Anguwar Abbatuwa dake cikin garin Abaji.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Yakubu ya ce lamarin yafaru ne 1:20 na dare lokacin da ƴanbindigar suka dirarwa gidan.

Ya ce masu garkuwar sun samu nasarar shiga gidan bayan da suka balla kofar shiga ciki.Inda ya ce bayan da suka gama bincike dakunan gidan ba tare da ganin mahaifin wanda suka yi garkuwa da shi ba ka wai sai suka yi awon gaba da matashin ya zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Ya kara da cewa ƴanbindigar sun gudanar da ta’asar ne ba tare da harba ko bindiga ba domin kada su ja hankalin makota.

Wakilin jaridar Daily Trust ya gano cewa mahaifin matashin da aka yi garkuwa da shi wanda ke sana’ar sayar da shanu da awaki na kokarin tuntubar masu garkuwar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like