Ƴan Taliban Za Su Tsagaita Wuta A Lokutan Bukukuwan Sallah


Kungiyar Taliban ta sanar da shirin dakatar da fada da sojojin Afghanistan na tsawon kwanaki uku domin bai wa al’ummar Musulmi damar gudanar da bukukuwan sallar azumi cikin kwanciyar hankali.

Wannan mataki ya kasance irinsa na farko da masu gwagwarmaya da makaman suka dauka cikin shekaru 17 da suka gabata, kuma ya zo ne kwanaki biyu bayan da shugaba Ashraf Ghani na Afghanistan ya sanar da shirin tsagaita bude wuta.

Sai dai kuma cikin sanarwar da suka bayar, ‘yan Taliban sun bayyana cewa za su ci gaba da kai hare-hare a kan’ yan kasashen waje a kasar, sannan kuma za su kare kansu idan an kai musu hari.

Shirin tsagaita bude wutar zai fara aiki ne daga ranar karamar sallah ta Eid el-Fitr.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like