Ƴan sanda sun yi holin wadanda suka yi garkuwa da shugaban hukumar UBEC


Rundunar ƴan sanda ta sanar da kama mutanen da suka yi garkuwa da shugaban hukumar UBEC, Mahmoud Abubakar.

An yi garkuwa da Abubakar tare da ‘yarsa ranar 29 ga watan Afirilu akan hanyar Kaduna-Abuja ya yin da aka harbe direbansa ya mutu nan take a wurin.

Watanni biyu bayan garkuwar, tawagar rundunar yan sanda ta musamman karkashin jagorancin,DCP Abba Kyari ta sanar da kama wani mai suna Abubakar Ahmadu wanda ya jagoranci wasu gungun mutane biyar da suka aikata laifin.

Har ila yau rundunar ta sanar da kama masu garkuwa da mutane,yan fashi,masu kera bindiga su fiye da 30.

Ga wasu daga cikin hotunan masu laifin da kuma makamansu:

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like