Ƴan sanda 7021 sun kamu da cutar Korona a Afrika ta Kudu


Jumullar yan sandan kasar Afrika ta Kudu, 7021 ne suka kamu da cutar Korona.

Bekhi Cele, ministan harkokin yan sandan kasar ne ya bayyana haka a yayin wani taro manema labarai a ranar Laraba.

Ya ce jami’an yan sanda 53 ne suka mutu a sanadiyar cutar da tayi sillar mutuwar mutane 4300 a fadin kasar.

A cewar kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN,Cele ya ce an killace yan sanda 4949 a babban birnin kasar Pretoria a yayin da aka kwantar da wasu 150 a asibiti.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like