Ƴan gudun hijira sun gudanar da zanga-zanga a Maiduguri


Jami’an ƴansanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa dubban yan gudun hijira da suka kwarara kan titunan birnin Maiduguri inda suke zanga-zanga kan halin kuncin da suke ciki a sansaninsu.

Karkashin jagorancin mata da kuma kananan yara masu zanga-zangar da suka fito daga Baga da Kukawa sunyi kira ga jama’a kan su kawo musu dauki.

Sun jawo tsawayar zirga-zirgar ababen hawa na tsawon wasu sa’o’i inda suka koka cewa sun shafe kwanaki 40 ba tare da ambasu abinci ba.

Akan babbar hanyar Bulunkutu masu zanga-zangar sun lalata allunan gwamnan jihar na yakin neman zaben kujerar sanata inda suka riƙa fadin “Bama so ku mai damu gida.”

Aisha Malum daya daga cikin mazauna sansanin ta bayyana cewa tun lokacin da suka iso daga Baga an a jiyesu a sansanin ba tare da abinci ba inda tace shinkafa kofi hudu kawai aka bata ita ƴaƴanta hudu cikin watanni biyu da suka wuce

Bukar Mala daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce wasu yan siyasa na bukatar sai ka nuna katin zabe kafin a barsu su shiga sansanin.


Like it? Share with your friends!

-1
75 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like