Wasu gungun yan fashi da makami sun farma wasu bankunan kasuwanci biyu dake garin Ile-Oluji inda suka kashe mutane hudu ciki har da yan sanda biyu.

‘Yan fashin sun yi amfani da nakiya inda suka fasa kofar banki na farko kafin su samu damar shiga ciki.

A cewar shedun gani da ido lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:00 kuma sun dauki tsawon mintuna arba’in suna cin karensu babu babbaka.

Sai dai yan bindigar sun gaza samun shiga cikin banki na biyu duk da cewa sun fasa kofar bankin da nakiya.