Ƴan BokoHaram Sun Kashe Sojoji 17 Tare Da Raunata 14.


Kamar yadda ta kafar yada labarai ta AFP a ranar Alhamis din da ta gabata ta bayyana cewa, ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai wani sabon hari a sansanin dakarun kasar nan,in da ya salwantar da rayukan soji 17 a jihar Borno.

Wannan shine hari na uku da ‘yan ta’addan suka zartar cikin sansanai daban-daban na dakarun cikin abinda bai wuci wata guda ba a birnin na Maiduguri da ya zamto wata farfajiya ta’addanci tun shekaru 9 da suka gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan sabon hari ya auku ne yayin da mayakan boko haram rike da muggan makamai cikin motocinsu na daukan kaya suka dirfafi sansanin dakarun sojin dake kauyen Garunda na jihar Borno a ranar Larabar da ta gabata.

Afkuwar wannan hari dai,na daya daga cikin munana na kwana-kwanan da ‘yan Boko Haram suka zartar a sansanan dakarun soji dake Najeriya, da hakan ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya a yankin gami da haskaka gwamnatin kasar sakamakon ikirarin ta na cewar ta nakasta ‘yan ta’addan tare da rusa su.

Kamar yadda wani dakarun soji ya shaidawa kafar watsa labarai ta AFP kuma ya bukaci a sakaye sunan sa ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun hallaka dakarun soji 17 tare da raunata 14 yayin aukuwar harin.

Baya ga wannan mugun lahani da ‘yan ta’addan suka yi a sansanin sun kuma arce da motoci da kuma makamai da dama.

A ranakun 14 da 26 ga watan Yulin da ya gabata ne ‘yan ta’addan suka kai makamancin wannan munanan hare-hare a sansanan dakarun soji dake kauyen Jilli na jihar Yobe da kuma wajen garin Maiduguri dake yakin Arewa maso Gabashin kasar nan.

Aukuwar wannan munanan hare-hare ta salwantar da rayukan dakarun soji da dama tare da muguwar ɓarna marar misali.

A yayin tabbatar da wannan lamari, hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta bayyana cewa, rayuwar wani ma’aikacin ta guda 1 ta salwanta yayin da yake gudanar da wasu aikace-aikace a sansanin dakarun sojin dake garin Damasak na jihar Borno.


Like it? Share with your friends!

1
74 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like