Ƴan bindiga sunyi garkuwa da ma’aikatan INEC hudu a jihar Benue


Wasu yan bindiga da ba’asan ko suwaye ba a jihar Benue sunyi garkuwa da wasu ma’aikatan hukumar zabe ta INEC su hudu.

Nentawe Goshwe, kwamishinan zabe na jihar ya tabbatarwa da manema labarai cewa lamarin ya faru ne a karamar hukumar Tarka ta jihar.

An gano cewa masu garkuwar sun karkatar da kayayyakin zabe tare da ma’aikatan dai dai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa inda aka turasu.

Jihar Benue na daya daga cikin jihohin Najeriya dake fuskantar rikicin siyasa tun bayan da gwamnan jihar,Samuel Ortom ya koma jam’iyar PDP daga APC


Like it? Share with your friends!

1
82 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like