Ƴar Gidan Dangote Zata Auri Dan Tsohon Shugaban Ƴan Sanda Na Kasa, M. D Abubakar


Shahararren dan kasuwan nan na Afrika Alhaji Aliko Dangote zai aurar da ‘yarsa, Fatima ga dan gidan tsohon shugaban ‘yan sanda na kasa marigayi MD Abubakar, wato Jamil.

Rahotanni sun nuna cewa za a daura auren ne a cikin watan Maris mai zuwa, imda auren zai samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen kasar nan. Inda ake sa ran hamshakin mai kudin duniya, Bill Gate zai halarci daurin auren.

Jamil dai direban jirgin sama ne, yayin da ita kuma Fatima babbar ma’aikaciya ce a kamfanin yin kek na “Cup Cake Factory”.

Wasu daga cikin wadanda ake tsammanin za su halarci shagalin bikin da za’ayi a otal din Eko dake Legas hadda attajirin me kudin Duniya, Bill Gates da kuma shugabannin kasashe daban-daban da tsaffin shugabannin kasa na Nijeriya dadai sauran manyan mutane masu hannu da shuni da kuma fada a ji.


Like it? Share with your friends!

-1
102 shares, -1 points

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like