Ƙungiyar TSINKAYA SOCIAL NETWORK A Jihar Jigawa Ta Amince Badaru Ya Zarce


Kungiyar Tsinkaya Social Network, Mai Kare Martabar Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar A Shafikan Sadarwa Na Zamani, Ta Amince Gwamna Badaru Ya Maimaita Kujerar Gwamnan Jihar Jigawa A Karo Na Biyu.

Shugaban Kungiyar Ne Malam Habu Badala Gumel, Ya Bayyana Haka Awurin Wani Taro Nuna Goyon Baya Da Kungiyar Ta Gudanar A Garin Gumel.

Shugaban Kungiyar Ya Cewa Za su Baiwa Gwamnatin Jihar Jigawa Karkashin Jagorancin Gwamna Badaru Dukannin Hadin Kai Da Goyon Baya Domin Ganin Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Dora Daga Inda Ta Tsaya A Zaben 2019.

Malam Habu Badala Gumel, Yace Kungiyarsu Ta Amincewa Da Tsarin Mulkin Sardaunan Ringim Gwamnan Jihar Jigawa Muhammadu Badaru Abubakar Da Yadda Yake Tafikar Da Mulkinsa Cikin Tsari Da Taka Tsantsan Da Dukiyar Al’umma Da Yadda Ake Budaddiyar Gwamnatu Mai Cike Da Daidaita Aiki Na Bai Daya, Da Wadannan Dalilan ne Kungiyar Ta Tsinkaya Ta yi Taronta A Garin Gumel Tsakanin Dukkanin Shugabanninta Na Jiha lDa Shugabannita Na Kananan Hukumomi 27 Dasuke Fadin Jihar Jigawa, Domin Nuna Amincewar su Akan Gwamna Badaru Ya Maimaita.

Daga Karshe Shugaban Kungiyar Malam Habu Badala Gumel, Ya Bada Tabbacin Cewar Kungiyarsu Ce Za ta Siyawa MGwamna Badaru Fom Din Sake Tsayawa Takarar Gwamna Jihar Jigawa A 2019.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like