Ƙungiyar NLC ta bukaci sojoji su gaggauta sako ma’aikatan jaridar Daily Trust


Ƙungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta bukaci a gaggauta sako ma’aikatan jaridar Daily Trust da wasu sojoji dauke da makamai suka yi awon gaba da su a Maiduguri.

A wata sanarwa dake dauke da sahannun shugaban kungiyar, Kwamared Ayuba Wabba wacce aka fitar ranar Lahadi da daddare, kungiyar tace babu wasu kalamai da za su gamsar wajen bayyana dalilin da suka jami’an tsaron suka dauki wannan matakin mai tsauri.

Ƙungiyar ta ce koda jami’an tsaron suna da sabani dake da nasaba da batun tsaron kasa to akwai hanyoyi da doka ta tanada da za abi wajen warware batun.

“Muna shawartar hukumomin sojoji da su gaggauta bada umarnin sako ma’aikatan da aka tsare da kuma bude ofisoshin jaridar da suka mamaye.”

A jiya ne dai mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu yace shugaban kasa Muhammad Buhari ya umarci sojoji da suka kawo karshen mamayewar da suka yi wa ofisoshin jaridar dake Abuja, Maiduguri da kuma Lagos.

Sojojin sun kai samamen ne kan babban labarin da jaridar ta buga a ranar Lahadi dake bayyana shirin da sojoji suke na kwato garin Baga daga hannun mayakan Boko Haram.


Like it? Share with your friends!

-1

You may also like