Ƙungiyar kwadago ta dakatar da shiga yajin aiki


Gamayyar kungiyoyin kwadago sun dakatar da batun tsunduma cikin yajin aiki da suka shirya farawa ranar Talata.

Ƙungiyoyin sun shirya tsunduma cikin yajin aikin domin neman a biya musu bukatunsu na karin mafi ƙarancin albashi.

A karshen zaman taron kwamitin nan mai wakilai daga bangarori uku da gwamnatin tarayya ta kafa,Ayuba Wabba shugaban kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ya fadawa manema labarai cewa matakin dakatar da tafiya yajin aikin a cimma shi ba ya da aka rattaba hannu kan wata yarjejeniya.

“Bayan da aka kawo wannan mataki aka kuma rattaba hannu akan yarjejeniya, yajin aikin da aka shirya shiga an dakatar da shi,” ya ce.

Yunkurin cimma yarjejeniya tsakanin kungiyar NLC da bangaren gwamnati ya samu koma baya a ranar Litinin bayan da dukkanin bangarorin biyu suka gaza cimma dai-daito kan mafi karancin albashi.

Bayan da suka shafe sama da sa’o’i 7 suna tattaunawa bangarorin sun cimma matsaya kan mabanbanta kudi yayin da kungiyar kwadago suka dage kan ₦30000 su kuwa tawagar gwamnti sun dage kan ₦24,000.

Taron ya cigaba har ya zuwa karfe 12 na dare inda dukkanin bangarorin suka cimma matsaya akan wani adadi da ba a bayyana ba a matsayin mafi ƙarancin alabashin.

Za dai a bayyana sabon mafi karancin albashi bayan an gabatarwa da shugaban kasa rahoton tattaunawa da misalin ƙarfe 4:15 na yamma.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like