LABARAI

Osinbajo Ya Tattauna Da Wasu Shugabannin AREWA


A jiya laraba ne Muk’addashin Shugaban K’asa Farfesa Yemi Osinbajo yayi wata muhimmiyar Ganawa da wasu Shugabannin al’umma dana addini daga yankin Arewacin Najeriya. 

Wadanda taron ya shafa  sun had’a da Shugaban Majalisar Dattawa ta K’asa Sanata Abubakar Bukola Saraki, Kakakin Majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara, shugaban kungiyar ACF Janar Magoro, Paul Onongo, Ango Abdullahi, Sheikh Bala Lau, Sheikh Dahiru Bauchi, Farfesa tsare, Sanata Wamakko. 

Sauran sun hada da Dakta Usman Bugaje, Rabaran Pam Yakubu, Paulin tallen, hafsoshin tsaro na sojojin sama, dana K’asa dana ruwa, ministan tsaro Mansur Dan Ali, sufeto janar na ‘Yan sanda, da kuma Shugaban Hukumar tsaron farin kaya ta DSS.

Comments

Latest

To Top