LABARAI

Dino Melaye Ya Saki Hotunan Wadanda Suka Kai Masa Hari


A ranar Litinin din da ta gabata ne, Sanata Dino Melaye  mai wakiltar Yammacin Kogi ya gamu da fushin wasu matasa a yayin da ya jagoranci zanga-zangar nuna rashin goyon baya ga gwamnan jihar, gwamna Yahaya Bello, inda wasu magoya bayan gwamnan suka farmake shi a gaban kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar, inda harin ya yi sanadiyyar rasa rayukan wasu mutum 5 daga cikin magoya bayan Dino, shi kuma yasha da kyar

Sanata Melaye ya mika alhakin harin da aka kai masa ga gwamnatin jihar inda ya fitar da wani rahoto akan shafinsa na sada zumunta mai taken:
‘Yan Ta’addan Yahaya Bello.

Comments

Latest

To Top