LABARAI

An Haramta Achaba A Wasu Garuruwan Jihar Kaduna


Sanarwa ta Fito daga Mai Bawa Gwamnan Jihar Kaduna shawara kan harkokin tsaro, Kanal Yusuf Yakubu Soja, inda ya ce majalisar tsaro ta jihar ta haramta hawa babur a wasu garuruwa da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin a samu saukin yawaitar satar mutane dake faruwa a yankunan. Masu Garkuwa Da mutane suna cin karen su ba babbaka a ‘yan kwanakin da suka gaba inda aka samu satar dan majalisa, malamin jami’a da kuma wasu dalibai. 

Comments

Latest

To Top